
Ministan shari’a kuma Antoni Janar na ƙasar nan, Abubakar Malami, ya ce kafin karewar wa’adin gwamnatin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari shekara mai zuwa,, ɗaukakar Najeriya zata dawo, zaman lafiya zai samu gindin zama. Malami ya ce shugaba Buhari na aiki tuƙuru da hana idonsa bacci domin tabbatar da komai ya koma kan hanya, ba miƙa mulki cikin ruwan sanyi ba kaɗai, har da tabbatar wa ƙalubalen tsaron da ya addabi ƙasa ya zama tarihi
Leave a comment