
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, Bola Tinubu, ya dauki mataimakinsa na zahiri a cewar jaridar Daily Trust. Jaridar ta ce bincikenta ya nuna mata cewa wanda Tinubun ya dauka, tsohon gwamna ne kuma tsohon sanata ne sannan Musulmi ne daga arewa maso gabashin kasar. Majiyoyin da jaridar ta tuntuba sun tabbatar mata cewa a cikin makon da za a shiga Tinubun zai sanar da mataimakin nasa a hukumance bayan ‘yan kwanakin da ya kwashe a kasar Faransa.
Leave a comment