Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) cikin kaskantar da kai ta amince da abubuwan da ke biyowa: cewa tana da nadama mai zurfi ga daukacin alhazan da suka shirya zuwa aikin Hajjin 2022 saboda wahalhalu da rashin jin dadi da suka samu a lokacin aikin jigilar jirage zuwa kasa mai tsarki. Hukumar ta yi irin wannan uzuri ga gwamnatin tarayyar Najeriya, da hukumomin jin dadin Alhazai na Jihohi, masu gudanar da yawon bude ido, da sauran jama’a kan duk wani abin kunyar da lamarin ya faru a makonnin da suka gabata. Abin takaicin shi ne, duk da kokarin da aka yi na jigilar dukkan maniyyatan Najeriya da ke son zuwa kasar Saudiyya don gudanar da aikin Hajjin 2022, NAHCON ta gaza wajen sauke wannan nauyi, musamman sakamakon koma bayan da aka samu a karshen makon da ya gabata da ya kawo cikas ga shirinta na kammala jigilar maniyyatan zuwa ranar 27 ga watan Yuni na wannan shekara. Sai dai abin takaicin shi ne, zabin jirage da aka yi hayar da ya baiwa hukumar NAHCON da kuma masu gudanar da yawon bude ido masu zaman kansu suma ya ci tura saboda asusunsu na IBAN ya gaza samun amincewar hukumomin Saudiyya.

Leave a comment