Gwamnatin Tarayya ta ce ba wai kawai ta na kokarin kawo karshen yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ke yi a halin yanzu ba, amma tana kokarin kawar da yajin aikin da kungiyar ke yi a nan gaba.
Gwamnatin ta bayyana hakan ne a taron koli karo na 81 na kwamitin ba da shawara kan harkokin ilimi (JCCE) da aka gudanar a Yola jihar Adamawa.
Sakataren dindindin na ma’aikatar ilimi ta tarayya, Andrew David Adejo, wanda ya zanta da manema labarai a gefen taron, ya jaddada cewa ana ci gaba da daukar matakai domin bai kamata ASUU ta koma yajin aiki nan gaba ba.
“Gwamnati na yin komai domin ganin ‘yan kungiyar ASUU sun dawo bakin aiki,” Adejo ya ce game da yajin aikin da ake yi a yanzu.
Leave a comment