Kwankwaso yace ana rufe jami’o’i da sauran makarantu na watanni, amma shugabanni su na kashe miliyoyi wajen sayen fam din takara Amma Babu ruwansu da harkar ilim.
A cewar Rabiu Kwankwaso, rashin fahimtar yadda za a jagoranci al’umma masu addinai da kabilu barkatai, ya sa Muhammadu Buhari ya lalata kasar nan. Kwankwaso ya ce rashin sanin aiki da rashin tausayi sun yi wa mutanen Najeriya mummunar illa. Haka zalika an samu karuwar rabuwar kai tsakanin jama’a. An rahoto ‘dan takaran yana zargin gwamnati mai-ci da zama sanadiyyar ta’azzarar rashin tsaro, tsadar rayuwa, rashin aikin yi da tabarbarewar ilmi da sauransu, ilim shine komai a Rayuwa.
Shiyasa nake bawa harkar ilim mahimmanci a duk lokacin da na samu dama zamu kawo gyara Dani da mataimakina Bishop Isaac inji kwankwaso.
Legit Nigeria Hausa
Me za ku ce?

Leave a comment