DA DUMI-DUMI:Buhari Ya Bawa ministan ilimi Wa’adin Sati Biyu ya kawo karshen Yajin Aikin ASUU
Published by
aminuasameen
on
Aminu Auwal saminu
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci ministan ilimi Mallam Adamu Adamu da ya warware yajin aikin da kungiyoyin jami’o’i hudu suka dade suna yi tare da kawo masa rahoto nan da makonni biyu.
Shugaba Buhari ya ba da umarnin ne a ranar Talata bayan da ya karbi bayanai daga ma’aikatu da hukumomin gwamnati da sassan da abin ya shafa wajen sasanta rikicin da ke tsakanin kungiyoyin jami’o’i.
Ku tuna cewa kungiyar malaman jami’o’i, ASUU, ta ci gaba da yajin aikin gargadi na wata daya a ranar 14 ga watan Fabrairu, kuma sauran kungiyoyin ma sun janye ayyukansu bayan hakan sakamakon gazawar gwamnatin tarayya wajen biyan bukatunsu.
Sauran kungiyoyin uku da suka fara yajin aikin sun hada da manyan ma’aikatan jami’o’in Najeriya, SSANU, kungiyar ma’aikatan da ba na ilimi ba, NASU da kuma kungiyar malaman fasaha ta kasa, NAAT.
Shugaba Buhari ya kira taron na ranar Talata domin karbar bayanai daga tawagar gwamnati kan yajin aikin ya dauki tsawon lokaci ana yi.
Shugaban bayan jin ta bakin masu ruwa da tsaki na MDA da abin ya shafa ya umurci Ministan Ilimi da ya tabbatar da cewa an warware matsalar cikin makonni biyu tare da kawo masa rahoto.
Leave a comment