An kara farashin fetur a fadin Najeriya gaba daya.

Sashin hausa na DW ya rawaito cewar A jihohin arewa maso yamma ana sa ran yanzu za a rika sayar da litar fetur kan kudi Naira 184, Naira 189 a yankin arewa maso gabas. Jaridar Daily Trust wacce ta ce ta samu tabbacin karin a Talatar nan, ta ce za a rika sayar da litar fetur a Naira 169 a Lagos, Naira 174 kuma a Abuja.
Leave a comment