Kungiyar malaman jami’o’i, ASUU, ta yi watsi da duk wani yunƙurin dakatar da yajin aikin da ta kwashe watanni shidda ta na yi. Ja

Jaridar daily nigerian ta rawaito cewar

Shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke ne ya yi wannan kiran a wani taron manema labarai a jami’ar Abuja, a jiya Talata.

Osodeke ya zargi ma’aikatar ƙwadago da samar da aikin yi, wanda Dakta Chris Ngige ke shugabanta da yin maƙarƙashiya wajen ci gaba da haifar da ruɗani a cikin tsarin sasantawa.

A cewar shugaban ASUU, kungiyar ba za ta taɓa dakatar da yajin aikin ba, sai dai ta tabbatar da kawo karshen yajin aikin na dindindin.

“ ASUU ta ce Ministan Ƙwadago da Aiki na taka babbar rawa a cikin rigimar da muke yi da gwamnatin Najeriya saboda wasu dalilai da ba za a iya kwatanta su ba.

“ Ngige tun da farko ya shaida wa duk wanda ya damu ya saurare shi cewa malaman jami’a ba shi su ke wa aiki ba, ya kuma shawarci kungiyar da ta yi tattaki zuwa ma’aikatar ilimi.

“‘Yan Najeriya na iya son sanin dalilin da ya sa ya maida kan sa a matsayin cikas ga warware rikicin da ke faruwa.”

Kungiyar ta ce ta ci gaba da mai da hankali kan burinta na ganin tsarin Jami’o’in Najeriya ya zama mai gogayya da na kasashen duniya.

Leave a comment

Quote of the week

"People ask me what I do in the winter when there's no baseball. I'll tell you what I do. I stare out the window and wait for spring."

~ Rogers Hornsby
Design a site like this with WordPress.com
Get started