Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce za ta samar da kudin tallafin man fetur da ya kai naira tiriliyan 6.72 a shekarar 2023

Jaridar The Nation a Najeriya ta ruwaito Ministar kudi, kasafi da tsare-tsare Hajiya Zainab Ahmed na bayyana haka a Abuja babban birnin kasar ranar Alhamis.

Hajiya Zainab ta ce gwamnati ta kiyasta cewa za ta samar da kudaden ne ta hanyoyi guda biyu kamar yadda yake kunshe a cikin kasafin kudin kasar.

A karkashin hanya ta farko, ministar ta ce ”An kiyasta cewa za a samar da tallafin tiriliyan 6.72 a shekarar 2023.

Ta kuma kara da cewa wadannan kudade kamfanin NNPC ne zai samar da su a madadin gwamnatin tarayya.

Leave a comment

Quote of the week

"People ask me what I do in the winter when there's no baseball. I'll tell you what I do. I stare out the window and wait for spring."

~ Rogers Hornsby
Design a site like this with WordPress.com
Get started