Hukumar NCDC mai yaƙi da cutuka masu yaɗuwa a Najeriya ta ce ta ƙaddamar da bincike kan wata baƙuwar cuta da ta ɓulla a Jihar Delta da ke kudancin ƙasar.

Rahotanni na cewa a makon da ya gabata wani ɗalibi ya rasu tare da kwantar da wasu tara a asibiti sakamakon cutar a yankin Boji-Boji na Ƙaramar Hukumar Ika ta Arewa-maso-Gabas.

BBC ta rawaito cewa, cikin wani saƙo da ta wallafa a shafinta na Twitter, NCDC ta ce tana sane da wata cuta da aka ce ta ɓarke tsakanin ɗaliban sakandare.

NCDC ta ƙara da cewa tana haɗa hannu da Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, da Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya, da kuma Ma’aikatar Lafiya ta Delta.

Leave a comment

Quote of the week

"People ask me what I do in the winter when there's no baseball. I'll tell you what I do. I stare out the window and wait for spring."

~ Rogers Hornsby
Design a site like this with WordPress.com
Get started