Bam ya tashi a hannun ‘yan bola jari a Bama ta Jihar Borno, mutum 9 sun mutu

Rahotonni sun bayyama cewa Akalla mutane tara ne suka mutu bayan tashin wani bam a karamar hukumar Bama da ke jihar Borno.

Rundunar hadin gwiwa ta farar hula da ta bayyana hakan cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 12:00 na rana a jiya Litini.

Ya ce mutane tara da abin ya shafa ‘yan saran karafa ne, baban bola, wadanda ke zaune a makarantar Sakandaren ‘yan mata ta gwamnati a Bama, wanda a yanzu sansanin ‘yan gudun hijira ne.

Bama na da tazarar kilomita 68 daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Majiya Alfijir hausa

Leave a comment

Quote of the week

"People ask me what I do in the winter when there's no baseball. I'll tell you what I do. I stare out the window and wait for spring."

~ Rogers Hornsby
Design a site like this with WordPress.com
Get started