Rahotanni sun tabbatae da cewar Mayakan Boko Haram da ‘yan bindiga na shirin kaddamar da farmaki kan babban Masallacin kasa, National Mosque da kuma Makarantar Horas da Lauyoyi da ke babban birnin Nijeriya, Abuja kamar yadda RFI Hausa ta rawaito.

RFI Hausa ta ruwaito jaridar Daily Nigerian na cewa  wata sahihiyar majiya ta shaida mata cewa, ‘yan ta’addan karkashin jagorancin Kachalla Ali Kawaje da Kachalla Dansadi na kitsa yadda za su sace malamai da dalibai daga Makarantar ta Horas da Lauyoyi da ke Bwari

Tuni ‘yan ta’adda suka nazarci tsare-tsaren tsaron da ke Makarantar domin sanin yadda za su kaddamar da farmakin da miyagun makamai  da suka hada da rokoki kamar yadda Daily Nigerian ta ambato.

Har ila yau, ‘yan ta’addan na shiirn dasa bama-bamai a kusa da harabobin Masallatai da Coci-coci da sauran wuraren al’umma. Majiyar ta ce, babban Masallaci na kasa, shi ke kan gaba a shirinsu na kaddamar da farmakin.

Leave a comment

Quote of the week

"People ask me what I do in the winter when there's no baseball. I'll tell you what I do. I stare out the window and wait for spring."

~ Rogers Hornsby
Design a site like this with WordPress.com
Get started