Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya gargadi ‘yan majalisar dokokin kasar da su bi a hankali kan matakin da wasu daga cikinsu ke yunkurin dauka na tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kwakwanso ya yi wannan gargadin ne jim kadan bayan ya kai ziyarar ban girma ga gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq a fadar gwamnati da ke Ilorin babban birnin jihar.

Kwankwaso, ya ce bai kamata Sanatocin su yi gaggawar girgiza shugaban ba, ko da yake ya ce “suna da dalilan da za su damu tun da batu ne na matsalar tsaro a kasar.”,

Kwakwanso, ya bukaci gwamnati da ta jajirce wajen tunkarar kalubalen rashin tsaro a fadin kasar nan.

Ya jaddada bukatar gwamnati ta tuntubi mutanen da ke da matukar damuwa kan matsalolin da ke addabar al’umma da nufin lalubo hanyoyin magance kalubalen.

Leave a comment

Quote of the week

"People ask me what I do in the winter when there's no baseball. I'll tell you what I do. I stare out the window and wait for spring."

~ Rogers Hornsby
Design a site like this with WordPress.com
Get started