Gwamna Ganduje da Sarki Sanusi sun yi kicibis a Abuja

A karon farko, Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya yi gaba-da-gaba da Sarkin Kano na 14 Muhammadu Sanusi II tun bayan da Gandujen ya sauke basaraken daga kujerar Sarkin Kano. Daily Trust ta ce mutanen biyu sun hadu ne a tashar jirgin sama ta Nnamdi Azikiwe a Abuja a Litinin din nan. Sai dai jaridar ba ta bayyana ko mutanen biyu sun yi musabaha kamar yadda aka saba kafin 2020, lokacin da aka sauke Sanusi daga mukaminsa ba.

Leave a comment

Quote of the week

"People ask me what I do in the winter when there's no baseball. I'll tell you what I do. I stare out the window and wait for spring."

~ Rogers Hornsby
Design a site like this with WordPress.com
Get started