Ƴan ta’addan da su ka kai hari kan jirgin ƙasa daga Abuja zuwa Kaduna sun sako ƙarin mutane biyar daga cikin fasinjojin da su ka yi garkuwa da su a ranar 28 ga Maris, 2022.

Daga cikin fasinjojin da aka ceto akwai Farfesa Mustapha Umar Imam, likita a asibitin koyarwa na Jami’ar Usman Dan Fodio (UDUS), Sokoto wanda a ka harba a sansanin ƴan ta’addan.

An harbi Imam ne lokacin yana tsare a hannun masu garkuwar, lamarin da ya haifar da damuwa game da lafiyarsa.

Sauran fasinjojin da aka sako sun haɗa da Akibu Lawal, Abubakar Ahmed Rufai, Muktar Shuaibu da Sidi Aminu Sharif.

Mawallafin da ke zaune a Kaduna, Tukur Mamu, wanda da kansa ya tsunduma cikin tattaunawa don ganin an sako wadanda lamarin ya rutsa da su, amma ya ja da baya saboda barazanar da ake yi masa a rayuwarsa ne ya tabbatar da sakin su ga jaridar Daily Trust a yau Talata.

Karin bayani na nan tafe…

Leave a comment

Quote of the week

"People ask me what I do in the winter when there's no baseball. I'll tell you what I do. I stare out the window and wait for spring."

~ Rogers Hornsby
Design a site like this with WordPress.com
Get started