Bayan an sake shi daga gidan yari, Dariye zai tsaya takarar Sanata

Tsohon gwamnan jihar Plateau, Sanata Joshua Dariye, zai bayyana sha’awar tsayawa takarar kujerar sanatan Plateau ta tsakiya a jam’iyyar Labour Party (LP).

A ranar Litinin ne aka sako Dariye ɗin, tsohon gwamnan Taraba, Jolly Nyame, da wasu mutane uku daga gidan yari watanni uku bayan afuwar da majalisar tsofaffin shugabannin ƙasa, karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi, a ranar 14 ga Afrilu, 2022.

Dariye, wanda aka yanke wa zaman gidan yari na shekaru 10 a kan zambar Naira biliyan 1.126, an sake shi bayan ya shafe kimanin shekaru huɗu a gidan yari.

Daily Trust ta tattaro daga majiya mai tushe cewa jam’iyar LP, reshen jihar Plateau, ta kammala shirye-shiryen karɓar Dariye daga Abuja domin karbar fom ɗin takarar sanata na jam’iyyar.

Dariye, wanda ya taba zama gwamnan jihar a jam’iyyar PDP ya fice daga jam’iyyar. Ya yi takara kuma ya lashe kujerar Sanata a 2011 a jam’iyar LP.

Wani jami’in jam’iyyar Labour, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce: “Eh, gaskiya ne shi (Dariye) zai tsaya takarar kujerar Sanata. Muna shirye-shiryen zuwan shi daga Abuja domin ya tsaya takarar Sanata”.

Majiyar ta ce Dariye zai ba da mamaki a zaben saboda kaunar da a ke masa a jihar.

Majiyar ta ce komawar Dariye ya kuma kara wa dan takarar gwamna na jam’iyyar, Patrick Dakum, wanda ya sauya sheka zuwa jam’iyyar Labour, bayan da ya kasa samun tikitin takarar jam’iyyar APC mai mulki karfi.

Leave a comment

Quote of the week

"People ask me what I do in the winter when there's no baseball. I'll tell you what I do. I stare out the window and wait for spring."

~ Rogers Hornsby
Design a site like this with WordPress.com
Get started