Daga Aminu Auwal saminu Gwamnatin jihar Katsina ta tabbatar da labarin satar kudi makudai da wasu da ba a kai ga sanin ko su wanene ba suka yi a ma’adanar kudi ta gidan gwamnatin jihar.
Darakta Janar na Gwamna Masari mai kula da kafafen sadarwar zamani Mal Al’amin Isah ne ya tabbatar da labarin, ga manema labarai, sai dai ya ce ba zai iya fadin ko nawa ne aka sace ba.
Majiyar Blueink ta rawaito cewa Mal Al’amin Isah ya ce tuni an kama wasu da ake zargi, su na ma tsare a hannun ‘yan sanda ana bincikensu.
Sai dai akwai rade-radin da ke yawo cewa kudin sun kai Naira milyan 31

Leave a comment