Tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau, zai bayyana ficewarsa daga jam’iyyar NNPP zuwa PDP, bayan wasu gwaɓaɓan alƙawura da ake zargin ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya yi masa.

Malam Shekarau, wanda ke wakiltar Kano ta tsakiya a majalisar dattawa, ya fice daga jam’iyyar APC zuwa NNPP a hukumance a wata wasika da shugaban majalisar, Ahmad Lawan ya karanta a zaman majalisar a ranar 29 ga watan Yuni.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta tattaro cewa Shekarau ɗin na samun tikitin kujerar Sanata a Kano ta tsakiya, kawai sai ya sumama zuwa Legas a ranar 24 ga watan Yuni domin ganawa da ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi domin ya zama mataimakin takararsa.

Jaridar ta kuma jiyo cewa tattaunawar da jam’iyyar Labour da Shekarau ke yi ta sha ruwa bayan da shugabannin APC da PDP suka fara kokarin ganin tsohon gwamnan ya dawo cikin su.

Yayin da shugabannin NNPP suka samu labarin ficewar Malam Shekarau, sai tawagar mutum 3 da suka haɗa da ɗan takarar gwamnan jihar na NNPP, Abba Kabir Yusuf, ɗan takarar kujerar Sanatan Kano ta Kudu, Kawu Sumaila da kuma ɗan takarar majalisar wakilai, Kabiru Rurum, suka nemi ganawa da shi a daren Juma’a a Abuja, amma Malam Shekarau ya ƙi ganinsu.

Kwamitin shura a ganawar sa ta ranar Lahadi da ya gabata s gidan Shekarau

Majiya mai tushe da ke da masaniya kan wannan shiri na sirri da Shekarau ke yi da kuma ganawar daban da dan takarar shugaban kasa na PDP Atiku Abubakar; abokin takararsa Ifeanyi Okowa da; Shugaban jam’iyyar na kasa, Iyochia Ayu, ta tabbatar da cewa tuni tsohon gwamnan ya “cimma yarjejeniya” da PDP kuma ana sa ran nan ba da daɗewa ba zai bayyana ficewar sa a hukumance.

A cewar majiyar, a ranar Lahadin da ta gabata ma, Shekarau ɗin ya kira taron gaggawa na majalisar shura kan harkokin siyasa, tare da sanar da ƴan majalisar halin da ake ciki.

DAILY NIGERIAN ta tattaro cewa wani kwamiti mai mambobi 21 zai yi zaman gana wa

Leave a comment

Quote of the week

"People ask me what I do in the winter when there's no baseball. I'll tell you what I do. I stare out the window and wait for spring."

~ Rogers Hornsby
Design a site like this with WordPress.com
Get started