Jami’an tsaro na sirri na DSS a Najeriya sun kama Tukur Mamu wanda ke shiga tsakanin ‘yan bindiga da wadanda aka yi garkuwa da su. Jaridar Premium Times ta ce Mamu ya shiga hannun DSS ne da isowarsa filin jirgin sama na Aminu Kano a Larabar nan. Kafin nan jami’an ‘yan sanda na kasa da kasa sun kama shi a kasar Masar, kafin daga bisani ya ce suka sake shi domin ba su same shi da wani laifi ba, ya kamo hanyar dawowa gida Najeriya.

Sai har yanzu tambayar ita ce me ya sa jami’an tsaron Interpol da na DSS suka kama shi?

Leave a comment

Quote of the week

"People ask me what I do in the winter when there's no baseball. I'll tell you what I do. I stare out the window and wait for spring."

~ Rogers Hornsby
Design a site like this with WordPress.com
Get started