
Malaman jami’o’in Najeriya na nuna damuwa kan yadda gwamnatin tarayya ta biya su rabin albashinsu na watan Oktoba.
A ranar 14 ga watan jiya ne malaman suka koma aiki, inda duk suka yi zaton bisa doka za a biya su cikakken albashin watan.
Watanni takwas ne suka kwashe suna yajin aiki a Najeriya, kafin kotu ta ba da umurnin su koma aiki.
Leave a comment