Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, a ranar Alhamis, ya amince cewa ya gaza a matsayinsa na Minista, saboda ya kasa magance ƙalubale da dama da ya kamata ya warware duk da kasancewarsa ministan ilimi mafi daɗewa.”
WMinistan ya ƙara da cewa, tun daga yaran da ba sa zuwa makaranta da suka ƙaru a lokacin da yake kan mulki zuwa ƙalubalen ASUU da sauran ƙalubalen da ke kawo cikas ga tsarin ilimin manyan makarantu, ya kasa samar da hanyar da ake buƙata.”
Ministan wanda ya yi magana a taron majalisar ilimi na ƙasa karo na 66 a Abuja a ranar Alhamis, ya kuma zargi ma’aikatun ilimi na jihohi da kara wasu abubuwan da suka taimaka masa wajen gazawarsa a matsayinsa na minista.”

Leave a comment