Shugabannin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya ASUU sun shiga ganawar sirri ta gaggawa.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa kungiyar ta shiga ganawar sirrin ne da tsakar ranar Litinin, a harabar sakatariyar kungiyar da ke jami’ar Abuja.
Ganawar karkashin jagorancin shugaban kungiyar Farfesa Emmanuel Osodeke, za ta duba batun biyan malaman rabin albashin watan Oktoba.

Leave a comment