Shugabar mata ta jam’iyyar APC ta kasa, Betta Edu, ta bayyana cewa Bola Ahmed Tinubu na da karfin da zai iya mayar da Najeriya babbar cibiyar tattalin arzikin duniya.

Ta yi wannan tsokaci ne a wani taro da kungiyar Mata Progressives Women Forum a Abuja, inda ta bukaci daukacin matan jam’iyyar da su fara hada-hadar goyon bayan dan takararta na shugaban kasa a 2023, Tinubu.

A cewar Edu, Tinubu ne ya fi kowa takara a zaben 2023 wanda zai iya gyara Najeriya.

Ta yi kira ga matan APC da su kunna kafafen sada zumunta na zamani don sayar da takarar Tinubu.

One response to “Tinubu zai mayar da Najeriya birnin tattalin arzikin duniya–shugabar matan APC”

  1. BUBA BURGASA Avatar
    BUBA BURGASA

    wannan ay fargar jeji ne.Watofa sun tabbatar da kasawar buhari kenan

    Like

Leave a reply to BUBA BURGASA Cancel reply

Quote of the week

"People ask me what I do in the winter when there's no baseball. I'll tell you what I do. I stare out the window and wait for spring."

~ Rogers Hornsby
Design a site like this with WordPress.com
Get started