Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya tsayar da farashin takin zamani, samfurin NPK kan Naira dubu 13 domin noman bana.

A jawabin da ya yi yayin ƙaddamar da shirin takin, Buni ya yi gargaɗi cewa iya manoma kawai za a sayar wa da takin.

“Ina mai gargadar ku cewa gwamnati ba za ta lamunci yin sama-da-faɗi ko kuma karkatar da takin ko ma zagon-ƙasa ba.

“Jami’an gwamnati da a ka amince da su sayar da kayan, su tabbata sun taba shi daidai a dukkanin Kananan Hukumomi 17 na jihar,” in ji shi.

Ya kuma yi kira ga manoma da kada su sayar da takin saboda sun same shi a farashi mai sauki.

One response to “Gwamnan jihar yobe ya kayyade farashin takin zamani kan naira dubu 13 a jiharsa”

  1. Ismail Yakubu ishaku Avatar

    Thanks god

    Like

Leave a reply to Ismail Yakubu ishaku Cancel reply

Quote of the week

"People ask me what I do in the winter when there's no baseball. I'll tell you what I do. I stare out the window and wait for spring."

~ Rogers Hornsby
Design a site like this with WordPress.com
Get started