Bello Turji, wanda Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara, ya yi wa afuwa, a yanzu haka yana kaddamar da farmaki kan ‘yan ta’adda a yankunan da suka mamaye domin tabbatar da cewa zaman lafiya da kwanciyar hankali ya dawo jihar.
Mataimakin gwamnan jihar Zamfara Sanata Hassan Nasiha ne ya bayyana hakan a yayin wani taro kan harkokin tsaro da kungiyar dalibai da wata jami’ar Madina ta shirya a Gusau babban birnin jihar.
Majalisar shura ta gindayawa shekarau sharudda biyar na sauya sheka zuwa PDP…
Cikakken labarin anan: https://trihausa.news.blog/2022/08/20/an-gindayawa-shekarau-sharu%c9%97%c9%97a-biyar-na-sauya-sheka-zuwa-pdp/
Hassan ya yabawa Turji bisa matakin da ya dauka na ajiye ayyukan fashi da makami, da kuma matakin taimakawa wajen samar da zaman lafiya a kananan hukumomi uku da ke kan gaba wajen fuskantar hare-hare ‘yan bindiga a jihar Zamfara.
A cewar mataimakin gwamnan, tun makwanni biyar da suka gabata ba a samu wata arangama tsakanin Fulani da Hausawa a kananan hukumomin Birnin Magaji, Shinkafi da Zurmi na jihar ba, sakamakon tattaunawar sulhun da aka yi tsakanin bangarorin biyu da ke rikici da juna a jihar.
Gidan talibijin na Channels ya ruwaito mataimakin gwamnan na cewa, kwamitin da Gwamna Bello Matawalle ya jagoranta ya gudanar da taron zaman lafiya da sansanonin ‘yan bin
diga tara a gundumar Magami da Masarautar Dansadau na kananan hukumomin Gusau da Maru na jihar domin su daina kai hare-hare ga mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.
Ya ci gaba da cewa, Turji wanda Gwamna Bello Matawalle ya yi wa afuwa, a yanzu haka yana kaddamar da farmaki kan ‘yan ta’adda a yankunan da suka mamaye domin tabbatar da cewa zaman lafiya da kwanciyar hankali ya dawo jihar.

Bello turji
Leave a comment